Gwamna mai barin gado ya naɗa sabbin shugabannin kananan hukumomi na rikon ƙwarya a jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ya naɗa ciyamomin ne domin cike gurbin da tsoffin shugabannin suka tafi suka bari bayan ƙarewar wa’adinsu A watan Nuwamba, 2023 aka yi zaben gwamna a jihar Kogi kuma ɗan takarar APC, Ahmed Usman Ododo ya samu nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum Jihar Kogi – Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya naɗa sabbin shugabannin ƙananan hukumomi na riko watau kantomomi a faɗin jihar. Gwamna Bello ya naɗa ciyamomin ne domin su kula da harkokin gwammati a mataki na uku wanda ya fi kusa da al’umma.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Mohammed Onogwu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Ya ce matakin da gwamnan ya dauka ya yi daidai da dokar da aka sake kafawa a jihar Kogi, wacce ta tanadi kafa tsari, al’amuran kudi, da ayyukan kananan hukumomi, 2023. Meyasa aka naɗa ciyamomin riko a Kogi? Sanarwan ta ce: “Gwamnan ya naɗa kantomomin ne da nufin cike gibin da tsoffin shugabannin kananan hukumomin suka tafi suka bari bayan sun kammala wa’adinsu wanda ya cancanci yabo.
“An zaƙulo ciyamomin ta hanyar mai tsafta kuma a tsanake duba da gogewa ga jajircewarsu, sun shirya tsaf domin tafiyar da harkokin kananan hukumomi cikin himma da azama.” Gwamnatin Yahaya Bello ta tsara cewa za a rantsar da sabbin shugabannin riƙon kwarya na kananan hukumomin a gidan gwamnati da ke Lokoja ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024. Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnan ya dakatar da dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Kogi daga aiki.
Sadiya Farouk ta yi wa EFCC bayani A wani rahoton kuma Hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta riƙe tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouk, ta kwana a hedkwata da ke Abuja. Wani jami’i ya bayyana cewa an samu ƙarin bayanai masu muhimmanci kan binciken da ake na ɓatan N37bn.
Leave a Reply